Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Wata Gwamnatin Jiha Ta Haramta Bukukuwan Kammala Karatun Ƙananan Yara, Ta Kafa Doka Kan Siyan Littattafai

Gwamnatin Jihar Imo ta sanar da dakatar da bukukuwan kammala karatu na yara masu zuwa kindergarten, nursery da ƴan JSS3 tare da umarni nan take daga Ma’aikatar Firamare da Sakandare, a wata sanarwa da kwamishinan ilimi Prof. Bernard Ikegwuoha ya fitar da aka sa wa kwanan watan ranar 15 ga Agusta, 2025.

A cikin sanarwar mai lamba MOEPS/COMMR/2025/VOL.1/155, an bayyana manufar dokar mai taken “Policy on Education for Public and Private Primary and Secondary Schools in Imo State” wadda za ta fara aiki nan take domin rage nauyin kuɗi kan iyaye da mayar da hankali ga karatun yara.

Kwamishinan ya ce ma’aikatar na son tabbatar da ilimi mai amfani ga duk ɗalibai, inda ya ce ‘Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare ta Jihar Imo na son samar da ilimi mai inganci ga dukkan ɗalibai’.

A cewar Ikegwuoha, daga yanzu sai ɗaliban Primary 6 da ɗaliban Senior Secondary ne za su samu damar gudanar da bukukuwan kammala karatu, yayin da ‘bukukuwa da liyafa na kindergarten, nursery da JSS3 aka soke su’ kamar yadda sanarwar ta tanada.

Har ila yau an umurci makarantun da su tsaya kan jerin littattafan da aka amince da su kuma a bari a yi amfani da su na mafi ƙarancin shekaru huɗu domin ƴan uwa su ma su iya sake amfani da littattafan, in ji kwamishinan.

Ma’aikatar ta yi gargaɗi ga makarantu masu zaman kansu musamman makarantun addini da su daina canza littattafai kowace shekara-shekara saboda hakan na jefa iyalai cikin damuwa, sannan za ta sa ido kan bin doka tare da ɗaukar matakin ladabtarwa ga duk wanda ya ƙi bin ƙa’ida.

Jama’ar Imo dai sun yi maraba da wannan tsari a kafafen sada zumunta inda mutane suka bayyana matakin a matsayin sauƙi daga wasu hanyoyin cin kuɗi na makarantu, amma masana suna ganin za a iya samun turjiya daga wasu makarantu masu zaman kansu kafin a ga cikakken amfanin tsarin.