Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Wata Kotu Ta Bayyana APC Da PDP A Matsayin Ƙaungiyoyin Ƴan Ta’adda Sai Dai PDP Ta Musanta

PDP ta ƙaryata rahotannin cewa wata Kotun Tarayya a Kanada ta ayyana PDP da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, inda gwamnatin tarayya ke shirin fitar da martani a yau, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mamba a Kwamitin Zartarwa, NEC, na PDP, Timothy Osadolor, ya shaida wa Daily Trust cewa kotun na da ƴancin ra’ayi amma hakan ba ya mai da iƙirarin da ta yi zuwa gaskiya: “babu abin da ke cikin ra’ayinsu da ya sa maganarsu ta zama ta gaskiya.”

Ya ce maimakon a yi wa duka jam’iyyun Najeriya kuɗin goro, ya kamata a nufi mutanen da ake dangantawa da ta’addanci musamman a cikin APC, yana mai zargin Kanada da “wuce gona da iri” ta hanyar haɗa PDP da jam’iyyar da “ta jawo wa Najeriya abin kunya.”

Osadolor ya bayyana hukuncin a matsayin ƙuri’ar rashin amincewa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa: “ba a danganta Tinubu da ta’addanci ba, amma rashin ƙwarewarsa wajen yaƙar shi (ta’addancin) ya bar ta’addancin na ƙaruwa, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na ƙoƙarinsa ya koma kan tsaron kujerarsa.”

Wani babban jami’in gwamnati ya shaida wa Daily Trust cewa za a fitar da martini daga ofishin harkokin wajen ƙasar nan “da zarar an tantance takardun hukuncin,” yana mai ƙari da cewa “muna sa ran jam’iyyun su kare kansu.”

A cewar takardun shari’ar da Daily Trust ta naƙalto, alƙalin kotun Phuong T. V. Ngo ya ce “ayyukan mambobin PDP, ciki har da manyan jiga-jigai, na tashin hankali da razana masu kaɗa kuri’a sun yi yawan gaske kuma sun daɗe suna faruwa fiye da yadda za a iya ware shugabancin jam’iyyar daga su.”

Masu sharhi sun gargaɗi cewa hukuncin na iya haifar da illa ga hoton Najeriya da kuma tsoratar da matasa daga shiga jam’iyyu, inda wasu ke kira da a ƙalubalance shi don kare darajar demokaraɗiyya.

Duk da haka, Daily Trust ta ce har yanzu ba a samu martanin APC ko na Ma’aikatar Harkokin Waje ba, alhali ɓangaren PDP na ganin wannan “faɗakarwa ce” ga Fadar Aso Rock don ta ɗauki batun da muhimmanci.