Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Makiyaya 12 A Sokoto

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetta Allah ta yi shelar cewar ‘Yan sa-kai a jihar Sokoto sun halaka mambobin ta 12 sakamakon wani farmakin da suka kai a matsugunansu da ke yankin Gwadabawa.

RFI Hausa ta rawaito cewa, shugaban kungiyar ta kasa Baba Usman Ngelzerma ya ce wannan rikici ya barke ne tun a ranar juma’ar da ta gabata sakamakon harin da tawagar ‘yan sa-kan suka kai matsugunan makiyayan, abinda ya kai ga rasa rayuka da kuma kona rugagen Fulanin.

Ngelzerma ya ce, matsugunan Fulanin da aka kaiwa hari sun hada da Tsola da Asara da Karan biki da kuma Sakamaro duka a yankin Gwadabawa, kuma an jikkata mutane da dama a yayin harin.

Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da barayin shanu, abinda ya sa wasu al’ummomi suka kafa kungiyoyin sa-kai domin taimakawa jami’an tsaro kare lafiya da dukiyoyin jama’a.

RFI Hausa ta kara da cewa, lokaci zuwa lokaci ana samun arangama tsakanin Fulani makiyayan da ‘Yan sakai abinda ke kaiga rasa rayuka.

Shugaban kungiyar Fulanin na kasa Baba Usman Ngelzerma ya bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen dakile wannan matsala da kuma hukunta duk wadanda aka samu da hannu a ciki.