Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yanda Ƴanbindiga Suka Kashe Liman Da Ƴaƴansa Biyu Da Jikansa Ɗan Shekara Biyu

Ɗan surukin tsohon babban Limamin Maru da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, Alƙali Salisu Suleiman, ya bayyana yanda ƴanbindiga suka kashe limamin tare da ƴaƴansa biyu da jikansa ɗan shekara biyu a hannun su bayan garkuwa da su.

Suleiman ya bayyana haka ne cikin wani bayani mai ban tausayi ga manema labarai, inda ya ce marigayin limamin, wanda tsohon alƙalin kotun shari’ar Musulunci ne, an sace shi tare da wasu mutane 23 a wani hari da ƴanbindiga suka kai a yankin.

Ya ce bayan makonni da dama da suka shafe a hannun masu garkuwar, an kashe su cikin tsananin mugunta, lamarin da ya girgiza al’ummar yankin da dangi baki ɗaya.

KARANTA WANNAN: Sama Da Mutum Dubu Sun Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa A Najeriya, Wasu Sun Mutu, In Ji NCDC

Suleiman ya ce, “ba wai kawai an kashe su ba ne, har ma da azabtarwa da wahala mai tsanani da suka sha kafin kisan, lamarin da ke nuna munin ayyukan waɗannan azzaluman ƴan bindigar.”

Wannan hari da kisan gilla ya sake jaddada yadda rashin tsaro ke cigaba da addabar yankin Arewa maso Yamma, musamman a jihar Zamfara da ke fama da hare-hare na garkuwa da mutane da kashe-kashe.

Mazauna Maru da dangin marigayin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin da sauran waɗanda suka rasa rayukansu bisa koyarwar addinin Musulunci, yayin da jama’a ke ci gaba da roƙon Allah ya kawo ƙarshen wannan masifa.