Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yanda Aka Raba Kuɗaɗen Da Aka Samu A Watan Nuwamba Tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi Da Ƙananan Hukumomi

Kwamitin Rarraba Kudaden Tarayya, FAAC, ya raba kuɗaɗen da aka samu a watan Nuwamba kimanin naira tiriliyan 1.088.783 ga Gwamnatin Tarayya, gwamnatocin jihohi da kuma ƙananan hukumomi.

Wannan ya bayyana ne a rahoton da kwamitin FAAC ya saki ranar Juma’a bayan kammala zaman tattaunawa.

Rahoton ya bayyana cewar kuɗaɗen da aka raba sun haɗa kuɗaɗen shiga naira biliyan 376.306, harajin kayayyaki na VAT naira biliyan 335.656, harajin tura kuɗaɗe a bankuna, EMTL, naira biliyan 11.952 da kuma harajin canjin kuɗaɗe naira biliyan 364.869.

Rahoton ya kuma yi nuni da karuwar kuɗaɗen shigar da aka samu a watan Nuwamba kan watan Oktoba da ya gaba ce shi.

A rahoton an kuma bayyana cewa, cikin naira tiriliyan 1.088.783 da aka samu, Gwamnatin Tarayya ta samu naira biliyan 402.867, sai kuma jihohi 36 suka samu naira biliyan 351.697, yayin da ƙananan hukumomi 774 suka samu naira biliyan 258.810.