Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

YANZU-YANZU: Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Ƙwace Nasarar Abba Gida-Gida Ta Bai Wa Gawuna Kano

Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Zaɓen Gwamnan Kano ta soke nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamnan Kano na ranar 18 ga watan Maris saboda aringizon ƙuri’u, inda ta bayyana Nasir Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda yai nasara.

Abba Kabir Yusuf wanda yai wa jam’iyyar NNPP takara a zaɓen, Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta, INEC ce ta bayyana shi a matsayin wanda yai nasarar cin zaɓen a wancan lokacin.

Bayan bayyana Abba a matsayin wanda ya ci zaɓen, abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Gawuna ya taya shi murna kafin daga bisani jam’iyyarsa ta shigar da ƙara.

A yau Laraba, alƙalan kotun su uku sun bayar da umarnin janye shaidar cin zaɓen Abba Kabir Yusuf da kuma miƙa shaidar ga Nasiru Yusuf Gawuna.

A lokacin yanke hukuncin, kotun ta soke ƙuri’u dubu 165,663 daga cikin ƙuri’un da Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen inda ta bayyana su a matsayin ba ingantattu ba saboda babu satamfi da sa hannu a jikinsu.