Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

YANZU-YANZU: DSS Sun Mamaye Ofishin SERAP

Ma’aikatan Hukumar Tsaro ta DSS sun mamaye ofishin kungiyar SERAP da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an sun nemi ganawa da shugabannin kungiyar kare hakkin dan Adam da lura da al’amuran tattalin arziki.

A cikin wani rubutu da aka wallafa a shafin X na SERAP, an bayyana cewa jami’an DSS sun mamaye ofishinsu ba bisa ka’ida ba.

Kungiyar ta bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya gaggauta umartar DSS da ta daina tsoratarwa da cin zarafin ‘yan Najeriya.