Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

YANZU-YANZU: Jirgin Sojan Saman Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja

Wani jirgin saman sojoji mallakin Rundunar Sojan Saman Najeriya, NAF, ya yi hatsari.

Jirgin dai ya tashi ne daga Kaduna yana kan hanyarsa ta zuwa Minna, babban birnin Jihar Neja lokacin da hatsarin ya faru.

Da yake tabbatar da lamarin, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojan Saman, Air Commodore Edward Gabkwet ya ce, jirgin ya bara Makarantar Firamare ta Zungeru a kan hanyarsa ta Kaduna, amma daga baya kuma aka gano cewar ya yi hatsari wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

KARANTA WANNAN: Gwamnatina Zata Magance Matsalar Tsaro A Najeriya – Shugaba Tinubu

Jirgin mai lamba MI-171 jirgi ne mai tashin angulu wanda akai nufin kai shi Kaduna domin gyara, ya yi hatsarin ne da misalin ƙarfe 1 na rana a ƙauyen Chukuba na Ƙaramar Hukumar ta Shiroro.

Gabkwet ya ce, ana ƙoƙarin ganin an ceto matuƙin jirgin da fasinjojin da ke kan jirgin, sannan kuma ana kan yin bincike domin gano musabbabin aukuwar haɗarin.