Hukumar Kula da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu biyu a lokacin da wani bene mai hawa biyu ya rufta a unguwar Noman’s Land, da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a Jihar Kano.
Dr. Nuraddeen Abdullahi, Ko’odinetan ofishin NEMA na Kano ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) faruwar lamarin.
Ya ce, “Hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe biyu na daren da ya gabata daga wani makwabcin wajen cewa wani bene mai hawa biyu ya rushe a unguwar Noman’s Land.
“Bayan samun wannan labarin, mun aika da tawagar ceto zuwa wurin da lamarin ya faru.
“An ceto mutane hudu da suka hada da miji, mata, da yara biyu; daga cikinsu, yaran biyu sun mutu, yayin da aka garzaya da ma’auratan asibitin Armed Forces Specialist Hospital, Kano, domin samun magani,” in ji Abdullahi.
Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da aikin ceto domin ganin an ceto mutanen da suka makale a cikin ginin.
Kamfanin NAN ya ruwaito cewa Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ‘Yansanda, Red Cross, NSCDC, SEMA, da sauran kungiyoyi suna cikin tawagar da ke aikin ceton.