Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

‘Yar Gombe Marar Hannaye, Mai Rubutu Da Yatsun Kafa Ta Samu Admission A Jami’a

Budurwa ‘yar shekara 22 da haihuwa mai suna Maryam Umar, wadda aka haifa babu hannaye ta roki ‘yan Najeriya masu jin kan al’umma, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu da su temaka mata wajen ganin ta kammala biyan kudin Jami’ar Jihar Gombe.

Takardar neman biyan kudin makarantar Maryam ta nuna cewa zata karanci ilimin Tsimi da Tanadi wato Economics a jami’ar, don haka zata biya kudin makaranta naira dubu 81,322.50.

Da take mika kokon bararta a tattaunawarta da manema labarai, Maryam ta ce, iyayenta ba su da karfin da zasu iya daukar nauyin ci gaba da karatunta, inda ta kara da cewa, yanzu haka ma da kudin sadaka take rayuwa.

WANI LABARIN: Mata 6 Da Aka Zaba A Matsayin Mataimaka Gwamnoni Masu Jiran Gado A 2023

Maryam ta ce, “Iyayena suna zaune ne a BCGA, Gombe. Na kammala secondary a 2022. Na ci maki 182 a UTME, sannan kuma ina credits 4 ciki har da English da Math a NECO.

“Amma ba ni da kudin da zan biya kudin rijista na karanatar Econonmics a Gombe State University. Iyayena ba su da kudi saboda haka ina rokon masu jin kan al’umma da su temaka min ta yanda ba zan rasa wannan damar ba.

Maryam ta kara da cewa gidansu suna da yawa, inda ta ce mahaifinta yana da ‘ya’ya takwas.

“Ni ce ‘ya ta uku, kuma ni kadai ce aka haifa babu hannaye. Ni ma zan samu ‘ya’ya takwas; Ina son na yi kasuwanci idan na gama karatuna,” in ji ta.

Ta kara da cewa, ta zabi ta yi kokari duk da nakasarta, inda ta ce yanzu haka ita take yiwa kanta komai ba tare da ta zama nauyi a kan kowa ba.

Maryam ta ce, “Ina jin farinciki ganin cewa ina karfin guiwa duk da nakasata, kuma duk abin da mai hannaye zai yi to nima zan iya yi da kafafuna.”

Ga masu son temakawa Maryam Umar ga lambar asusunta na Union Bank: 0015749904.