Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yaro Dan Shekara 17 Ya Lalata Kananan Yara Biyu A Kano – ‘Yansanda

Wani yaro dan shekara goma sha-bakwai ya shiga hannun ‘yansanda a Jihar Kano bayan an zarge shi da lalata kananan yara biyu.

Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kano, Mamman Dauda ne ya tabbatar da kama yaron a tattaunawar da yai da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN a yau Laraba.

“A ranar 2 ga watan April, da misalin karfe 3 na rana, ‘yansanda sun samu korafin zargin cewa wanda ake zargin ya yaudari yaran su biyu, ‘yan shekara bakwai da shekara shida zuwa dakinsa da ke Unguwar Badawa Layout a Kano.

“Wanda ake zargin ya yaudare su ya kuma yi lalata da su. Tuni aka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin Koyarwa na Abdullahi Wase da ke Kano domin ba su maganin.

“Ana ci gaba da bincike kan lamarin, yayinda binciken kuma ya kammala za a mika yaron zuwa kotu,” in kwamishinan ‘yansandan.

NAN