Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yau Majalissar Dattawa Za Ta Yanke Hukuncin Ƙarshe Kan Ƙudirin Gyaran Haraji Da Ke Ci Gaba Da Jawo Cece-Kuce

Shugabannin majalisar dattawa sun ɗage amincewa da ƙudurorin gyaran tsarin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura zuwa yau Laraba domin samun cikakkiyar tantancewa da muhawara, in ji rahoton PUNCH.

Waɗannan ƙudurori guda huɗu da suka haɗa da Nigerian Tax Bill, Tax Administration Bill, Revenue Tax Board Bill da Nigerian Revenue Service Establishment Bill, an aike da su majalisar ne watanni shida da suka gabata don sauya tsarin tattalin arziƙin ƙasa da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga, abin da ke ci gaba da jawo cece-kuce.

Tuni majalisar wakilai ta amince da su makonni biyu da suka gabata, lamarin da ya ƙara matsin lamba kan majalisar ta dattijai.

WANI LABARIN: Sule Lamido Zai Ƙaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwarsa

A yayin zaman majalisar na ranar Talata, an kuma yanke shawarar gudanar da wani babban taron ƙasa na kwanaki biyu kan matsalolin tsaro da suka addabi ƙasa, bayan gabatar da ƙudiri daga Sanata Jimoh Ibrahim na jihar Ondo.

A cewarsa, “matakin tashin hankali na duniya ya samo asali ne daga rikicin Rasha da Ukraine, da kuma saɓani tsakanin arewacin duniya da kudanci,” yana mai bayyana yadda hakan ke ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci da gagarumin tasiri kan cimma manufofin ci gaba na duniya.

Ya ƙara da cewa, “Yaƙin tattalin arziƙi da ake yi a duniya na ci gaba da ingiza rikice-rikice, kuma yana buƙatar sabbin hanyoyin yaƙi da ƙarin kuɗaɗe ga rundunonin tsaro.”

A ƙarshe, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya amince da ƙudurin gudanar da zaman taron tsaro na kwanaki biyu a Abuja tare da kafa kwamitin wucin gadi don shirya taron, wanda zai haɗa da wakilai daga matakan gwamnati daban-daban da kuma sarakunan gargajiya.