Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Yau Tinubu Zai Tura Sunayen Sauran Ministocinsa Ga Majalissar Dattawa

Jaridar PUNCH ta gano cewar a yau Laraba ne, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tura sunayen sauran mutanen da yake son ya naɗa ministoci zuwa ga Majalissar Dattawa.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya daga Majalissar Dattawa ta tabbatar da cewa, sunayen ƙarin ministocin Tinubu zai isa majalissar a daren jiya Talata ko da sanyin safiyar yau Laraba.

Majiyar ta kuma ce, a yau ne Shugaban Majalissar Dattawa, Godswill Akpabio, zai karanta sunayen ƙarin sunayen ministocin, sannan kuma a yau ɗin ne majalissar zata ƙarƙare tantance mutane 28 da Shugaba Tinubu ya tura mata.

A ranar Litinin da ta gabata ne, sanatocin suka tantance mutane 14 cikin 28 da aka tura musu, sai kuma jiya Talata inda sanatocin suka tantance mutane 9 daga cikin sauran 14, wannan ya nuna a yau zasu tantance sauran mutane 5 da suka rage, sannan su fara shirin tantance sabbin sunayen da zasu karɓa a yau.