Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Zaɓen Cike Gurbin Kaura-Namoda Ta Kudu A Zamfara Bai Kammala Ba (Inconclusive), INEC Ta Faɗi Dalilai

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ayyana zaɓen cike-gurbin Kaura-Namoda ta Kudu a Zamfara a matsayin inconclusive bayan da tazarar ƙuri’u tsakanin manyan jam’iyyun ta gaza kai wa adadin PVCs da aka karɓa a rumfunan da aka soke.

Mai bayyana sakamakon zaɓe a mazaɓar, Farfesa Lawal Sa’adu na Jami’ar Tarayya ta Gusau, ya ce an soke zaɓe a yankuna biyu, Sakajiki da Kyambarawa, bisa dalilan da suka shafi ƙa’idoji.

A Sakajiki (lamba 06), rumfuna biyu da masu rajista 1,357 da PVC 1,298 lamarin ya shafa; a Kyambarawa (lamba 05), rumfuna uku da masu rajista 4,088 da PVC 1,964 abin ya shafa, jimillar masu rajista 5,446 da PVC 3,265.

Sakamakon wucin-gadi ya nuna APC na kan gaba da ƙuri’u 7,001 yayin da PDP ke bi mata da ƙuri’u 5,339, tazarar 1,662, ƙasa da PVC 3,265 na rumfunan da aka soke.

Farfesa Sa’adu ya ce, yana dogaro da “Sashe na 24 (2 & 3), 47 (3) da 51 (2) na Dokar Zaɓe ta 2022,” saboda haka “an ayyana zaɓen a matsayin inconclusive.”

A gefe guda, APC ta yaba wa masu kaɗa kuri’a, tana mai cewa zaɓen ya kasance “mai tsauri, cike da tashin hankali,” tare da iƙirarin cewa gwamnati ta “tsoratar da jama’a,” duk da haka “mutane sun nuna jajircewa.”

Jam’iyyar ta yi kira da a kwantar da hankali, amma ta gargaɗi cewa “duk wani yunƙuri na sauya amanar jama’a za ta matuƙar ƙalubalance shi.”