Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Za A Ci Gaba Da Tsare Waɗanda Ake Zargi Da Ƙaryar KAROTA Su 25 A Kano

Wato Kutun Majistare a Kano jiya Talata, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani da ake kira Aminu Salisu da wani Kamilu Yusuf da kuma wani Baba Jibril da sauran wasu mutane 22 waɗanda aka kama suna mallakar takardun bogi na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababan Hawa ta Kano, KAROTA.

Da ake gurfanar da waɗanda ake zargin a Babbar Kotun Majistare gaban Alƙaliya Halima Wali kan zarge-zargen aikata laifuka guda uku, Mai Shigar da Ƙara, Tijjani Ibrahim ya faɗawa kotun cewa, waɗanda ake zargin sun aikata laifukan ne da gangan a ranar 22 ga watan Yuli, 2023.

Wani Labarin: An Ƙara Kama Emefiele Kan Zargin Ta’addanci

Ya ƙara da cewa, laifukan da suka aikata ya saɓa da Sassa na 97, 393, da 321 na Kundin Manyan Laifuka, sai dai kuma da aka karanta musu zargin da ake yi musu, waɗanda ake zargin sun musanta aikata laifukan.

Lauya mai kare waɗanda ake zargin, Nazifi Rabiu, ya roƙi kotun da ta bayar da su beli duba da Sassa na 35 (6), da 36 (5) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya wanda aka sabunta, da kuma Sashi na 171 (3) na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Kano na 2019.

Alƙaliyar Kotun, Halima Wali, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa gobe Alhamis 27 ga watan Yuli domin yanke hukunci kan buƙatar neman belin.