Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Za A Cigaba Da Dambarwa Tsakanin Ƴanƙwadago Da Gwamnati Ranar Talata Kan Mafi Ƙarancin Albashi

Tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi a Najeriya zata cigaba a ranar Talata mai zuwa a daidai lokacin da ake cigaba da musayen maganganu tsakanin jami’an gwamnati kan abun da ya faru a farkon makon nan inda gwamnati ta nuna zata bayar da naira 48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Ita dai Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta jaddada matsayarta ta cewar, ba zata yarda da duk wani abu da yake ƙasa da naira dubu 615,000 ba a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Shugaban Kwamitin Tattaunawa kan Mafi Ƙarancin Albashi, Alhaji Bukar Goni ne ya sanar da sanarwar cigaba da tattaunawar a wasiƙar da ya aikewa ƴanƙwadagon mai ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Mayu, 2024.

A zaman da ya gabata dai, Ƙungiyar Ƙwadago, NLC da Ƙungiyar Ƴankasuwa, TUC sun fice daga ɗakin tattaunawa kan samar da mafi ƙarancin albashin da wakilan gwamnati, bayan ɓangaren gwamnatin sun gabatar da cewar a amince da naira 48,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

A yayin da gwamnatin ke miƙa buƙatar a amince da naira 48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ne, su kuma masu kamfanoni masu zaman kansu suka nuna cewar zasu biya naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.