A daidai lokacin da watan Ramadan na shekarar Musulunci ta 1444 ke karewa, Majalissar Koli ta Al’amuran Addinin Musulunci a Najeriya, NSCIA, karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ta bukaci Musulmi a duk fadin Najeriya da su fara duba sabon watan Shawwal a ranar Alhamis mai zuwa.
Daraktan Mulki na NSCIA, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya saki a yau Talata.
“Biyo bayan shawarar Kwamitin Ganin Wata na Kasa, NMCS, Mai Alfarma Sarkin Musulmi na kira ga al’ummar Musulmi da su fara duba sabon watan Shawwal, 1444 da zarar rana ta fadi a ranar Alhamis 29 ga Ramadan, 1444 wadda zata zo daidai da 20 ga watan Afrilu, 2023.
“Idan har aka ga watan kamar yanda tsarin Musulunci ya nuna da kuma hanyoyin tantancewa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai bayyana Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal, 1444 kuma ranar karamar sallah.
“Haka kuma idan ba a samu ganin watan a wannan rana ba, Asabar 22 ga watan Afrilu, 2023 zata zama ranar karamar sallah ba tare da wata tantama ba,” in ji Usman-Ugwu.
Ya kuma yi kira ga Musulmi da kuma jagororin Musulmai a fadin Najeriya da su sanar da NMSC sahihan labaran ganin watan Sahawwal, 1444.