Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta yi ƙarin haske a kan dalilanta na ɗage zaman tattaunawa da ta shirya da Sheikh Idris Abdul’aziz, wanda ake zargi da munana kalamai a kan Annabi Muhammadu.
Tun farko a yau Asabar ne, hukumar ta shirya gudanar da muhawara da malamin addinin Musuluncin, sai dai sa’o’i kafin lokacin sai ga wata sanarwa da ke cewa an ɗage zaman.
Ana zargin fitaccen malamin ne da furta kalamin cewa ‘ba ya buƙatar taimakon Annabi’, abin da mafi yawan mutane ke gani, munana lafazi ne ga Fiyayyen Halitta.
Lamarin ya janyo muhawara mai zafi da ka-ce-na-ce har a tsakanin malaman addinin Musulunci da ke arewacin Najeriya, inda wasu suka fara kiraye-kirayen lallai hukumomi su ɗauki mataki.
Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Bauchi ta ce abin da ya sa ta ɗage zaman shi ne a bayar da dama ga malamin, da kuma sauran malaman da za su yi muhawarar, har ma da hukumomi, duk su shirya.
“Duk lokacin da ake so za a yi wani zama, da wani malami domin a tuntuɓe shi bisa ga bayanan da ya yi, ana buƙatar ka yi wani tsari na musamman na yadda za ka ba wa mutum dama, ya faɗi haƙiƙanin abin da yake nufi,” in ji Mustafa Baba Illelah, shugaban hukumar.
Ya ce matakin kuma zai ba da damar “A samu malamai sanannu kuma ƙwararru a fannin da ake magana a kai, to wannan ya sababba, lokacin da aka sa, a kan yau za a yi, da sauran shirye-shirye da kuma wasu dalilai, suka sa muka ga dacewar a ɗaga zuwa wani lokaci “.
A cewar Mallam Mustafa, komai yana buƙatar tsari, yadda za a tsara wurin da za a yi zaman.
“Yana da kyau mu samar da irin abubuwan da ake buƙata, don wanda za a yi irin wannan zaman da shi.”
‘Ba Zama Irin Na Titi Ba Ne’
Mallam Mustafa Baba Illelah ya nanata cewa ba don Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi suka ɗage zaman a ranar Asabar ɗin nan ba.
Zama ne da ke buƙatar a yi tsari, da ba da tsaro ga kowanne ɓangare, in ji Mallam Mustafa. “Ba zama ne kawai da za a je, a yi kamar a bakin titi ba”.
Akwai buƙatar mu ba shi tsaro. Mu ba shi kariya, a cewar shugaban hukumar shari’ar ta Bauchi.
Haka zalika, su ma malaman sai an tanadi wurin da zai ba da damar ba su tsaro da kariya, don gudanar da zaman cikin kwanciyar hankali, ya ƙara da cewa.
A ranar 10 ga watan Yulin shekara ta 2021, gwamnatin Kano ta shirya irin wannan muƙabala da Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a jihar.
An dai zargi malamin na Kano ne da furta kalaman saɓo a kan Annabi Muhammadu (SAW), abin da ya janyo daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu.
‘Ko Dai Fasawa Aka Yi’
Sai dai bayan fitar sanarwar da ke bayyana ɗage zaman muhawarar a shafukan sada zumunta, wasu sun yi ta raɗe-raɗin cewa an dakatar da zaman ne gaba ɗaya.
Sai dai Mallam Mustafa Baba Illelah ya ce ba shakka mutane za su yi ta maganganu iri daban-daban a kan wannan batu. “Amma mu dai mun san dalilanmu.
Kuma Allah ya san dalilan da suka sa muka ɗage”.
Shugaban Hukumar Shari’ar ya ce: “Mutane kuma maganganunsu… Za ka ji maganganu (kan dalilan ɗagewar) fiye da goma”.
Ya ƙara da cewa ba za su fasa yin muhawarar ba, kamar yadda wasu ke hasashe.
“In mun fasa ne gaba ɗaya, sai mu fito fili mu ce mun fasa. Amma, ba mu faɗi haka ba,” in ji malamin.
Akan Me Za A Yi Muhawarar?
Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ya ce sun shirya zaman muhawara ne game da wata “Ibara ko jimla da malamin ya faɗe ta a cikin bayanansa.
A cikin tafsirinsa ne! Yana kore batun (cewa) ba ka neman taimako, in ba a wajen Allah (Tabaraka Wa Ta’ala) ba.
Ya ambaci sunayen waɗansu shehunan malamai da ba a neman taimakonsu”.
“To, daga ƙarshe, shi ne ya nuna cewa ko Manzon Allah (SAW) ma, ba za ka nemi taimakonsa ba, ko ba ya buƙatar taimakonsa”, in ji Mallam Mustafa.
Ya ce wannan jimla ce ta ɗauki hankalin al’umma kuma abin da ya sa kenan aka ba da dama ga malamin don ya je ya yi bayani game da kalmar da ya faɗa.
“Ya zo ya yi bayani bisa ga wannan kalma da ya faɗa. A ji madogararsa.
Da kuma shin ya inganta mutum, yana iya faɗin haka wa Manzo (SAW)? Ko kuwa hakan akwai aibi a cikinsa?” Mallam Mustafa ya ƙara da cewa.
Shirin Da Hukumar Ta Yi Zuwa Yanzu
Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi ta ce tuni ta kammala muhimman tsare-tsare don wannan muhawara da za a yi da Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi.
“Mun tsara komai”.
Duk da yake, hukumar ba ta bayyana wa BBC wurin da za a yi muhawarar, da kuma malaman da za su yi muhawara da Sheikh Idris Abdul’aziz ba. Amma dai ta ce ta yi dukkan muhimman tanade-tanade.
Mun samar da wurin da za a zauna, in ji Mallam Mustafa. “Mun samar da malaman da zai tattauna da su”.
Ya ƙara da cewa, an tanadi malamin da zai jagoranci tattaunawar wato wanda zai shugabanci zaman.
Haka zalika, hukumar ta ce ta tanadi hatta jami’in da zai kiyaye lokaci a duk sa’ar da sauran shirye-shiryen suka kammala don wannan muhawara.
‘Dutsen Tanshi Ya Karɓi Gayyata Hannu Bi-Biyu’
Shugaban Hukumar Shari’a ta jihar Bauchi ya ce da aka kai wa Sheikh Idris Abdul’aziz takarda, ya karɓi gayyatar da sakakkiyar fuska, kuma ya sa hannu a kan takardar amsa goron gayyata.
“Duk ya yi wannan.
Ya karɓe ta da hannu bibbiyu. Kuma ya amsa a kan zai zo (wurin muhawarar)”.
Mallam Mustafa Baba Illelah ya ce Sheikh Idris Abdul’aziz ya amsa zai zo, don ga shi ya bayar a rubuce.
Kuma ga shi kamar yadda aka yi ta gani a soshiyal midiya, in ji shugaban shari’ar cewa ya amsa gayyata.
“Kuma in Allah ya yarda zai zo,” Mallam Mustafa ya tabbatar wa BBC.
BBC HAUSA