Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

‘Zai Iya Zamewa Yaƙi,’ Burkina Faso Da Mali Sun Goyi Bayan Sojojin Nijar Sun Kuma Gargaɗi ECOWAS

Sojojin da ke mulki a Burkina Faso da Mali sun yi gargaɗi kan yunƙurin amfani da ƙarfin soji a kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, inda suka ce yin hakan tsokanar yaƙi ce a Afirka ta Yamma.

Gargaɗin wanda ya zo a wata sanarwar haɗin guiwa da ƙasashen biyu suka fitar ta biyo bayan gargaɗin da Shugabannin Afirka ta Yamma suka yi kan Nijar.

A zaman da tai a makon da ya gabata, Ƙungiyar Ci Gaban Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta yi gargaɗin ɗaukar matakin soja kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a makon da ya gabata.

A zaman da Shugaban Ƙungiyar, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta, ECOWAS ta bai wa masu mulkin soja a Nijar wa’adin kwanaki bakwai da su dawo da Shugaban Ƙasa Mohammed Bazoum kan karagar mulkinsan ko su fuskanci ƙarfin soja.

Da suke nuna baƙin cikinsu da sanarwar, ƙasashen Burkina Faso da Mali a daren jiya, sun buƙaci Shugabannin Afirka ta Yamma da su ƙyale Nijar, inda suka jaddada cewa, duk wani motsin nuna ƙarfi da za ai to zai iya jawowa babbar ɓarna.