Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Zamfara: Ƴan Bindiga Sun Kashe Waɗanda Suka Kama Bayan Sun Karɓi Kuɗin Fansa Sama Da Naira Miliyan 50

Al’umma a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun shiga cikin alhini bayan da aka kashe mutane 38 da aka sace musu, duk da cewa an biya ƴan bindigar sama da naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Shugaban ƙaramar hukumar, Mannir Haidara Kaura, ya tabbatar da cewa an sace mutum 56 daga ƙauyen, inda daga bisani aka sako mutum 18 da suka koma gida da raunuka.

Ya ce an kwantar da waɗanda aka sako a asibiti domin samun kulawar lafiya, tare da shirin kai gaisuwar ta’aziyya ga iyalan waɗanda aka kashe.

WANI LABARIN: Niger: Haɗakar Rundunar Tsaro Ta Hallaka Ƴan Bindiga Da Dama A Ƙaramar Hukumar Shiroro, Ta Kuma Rasa Jami’ai

“Daga bayanan da na samu a matsayina na shugaban ƙaramar hukuma, 56 aka sace kuma 18 ne suka dawo,” in ji shi.

Wani mazaunin ƙauyen, Ibrahim Banga, ya ce an daɗe da sace mutanen tun watannin da suka gabata, inda ƴan bindigar suka nemi naira miliyan ɗaya kan kowannensu.

“Mun tara kuɗin fansa muka ba su, amma daga ƙarshe mutum 18 kacal suka sako mana,” in ji Banga, wanda ya ƙara da cewa waɗanda aka sako sun ba da labarin yadda aka yi wa sauran mutanen kisan gilla ɗaya bayan ɗaya.

Ya roƙi gwamnatin tarayya da ta Jihar Zamfara da su ɗauki matakin gaggawa ta hanyar tura sojoji domin dawo da zaman lafiya da kuma ceto waɗanda har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.