Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa tsaro da sake ƙwace dazukan da ƴan bindiga da ƴan ta’adda suka mamaye musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda ya ce “zamu zuba jari a fannin fasaha mu ƙwace dazuka,” a jawabinsa ga dattawan Katsina yayin liyafar da aka shirya masa a gidan gwamnatin jihar ranar Juma’a da dare.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar mai taken “Zamu tsare dazukanmu mu ƙarfafa leƙen asiri a Arewa maso Yamma, in ji Shugaba Tinubu.”
A cewar wani bincike da UNIDIR ya gudanar, harin ƴan fashi da makami ya ƙaru da kashi 731 daga 2018 zuwa 2022, inda aka kashe mutane 8,300 aka kuma sace wasu 9,527 daga 2019 zuwa watanni uku na farko na 2024, inda hakan ya shafi kusan kashi 62 cikin 100 na duk sace-sacen da aka yi a ƙasar.
WANI LABARIN: An Gano Fiye Da Naira Biliyan 80 A Asusun Wani Shugaban NNPC
A watan Yuni 2024 kaɗai, RouteWatch ta ce an kai hare-hare 277 a jihar Katsina, inda aka rasa rayuka 684, sai kuma harin ranar 8 ga Afrilu 2025 a ƙauyukan Layin Gara da Maikuma wanda ya kashe mutane shida aka kuma yi garkuwa da 59.
Shugaban ƙasa ya ce “zuba jari baya zuwa inda ake da ƴan bindiga da ta’addanci,” yana mai jan hankalin cewa dole ne a magance matsalar tsaro idan ana son jawo sanya hannun jari a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa waɗanda rikice-rikice suka shafa, tare da niyyar faɗaɗa filin jirgin saman jihar Katsina don samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.
A nasa ɓangaren, tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya faɗa wa Tinubu cewa, “Kana da ƙarfin hali da hangen nesa wajen fuskantar ƙalubalen ƙasar nan. Idan mutum ba shi da ƙarfi da jajircewa, ba zai iya jure sabbin tsare-tsare da sauye-sauyen da ake buƙata ba. Kuma ni na san zaka iya, kana da ƙarfin hali.”