Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Zan Goyi Bayan Peter Obi A 2027 Matuƙar Haka PDP Ta Tsara, In Ji Atiku

Ɗantakarar Shugaban Ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin tutar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce, idan a zaɓen shekarar 2027 jam’iyyarsa ta yanke cewar zata fitar da ɗantakara daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ne kuma ta zaɓi Peter Obi a matsayin ɗantakarar to zai goya masa baya.

Atiku ya ce, ya sha faɗa tun kafin ma zaɓen 2023 cewar, idan PDP ta miƙa takara zuwa yankin Kudu musamman ma Kudu maso Gabas to shi ba zai tsaya takara ba, matuƙar wannan ita ce matsayar jam’iyyar.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa da aka saki kwanan nan biyo bayan ziyarar da Peter Obi ya kai masa, inda kuma ya ƙara da cewar, haɗaka tsakanin jam’iyyar PDP da Labour Party abu ne mai yiwuwa.

Ya ƙara da cewar, mambobin jam’iyyarsa ne zasu yanke makomarsa game da takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Ganawar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar da Peter Obi dai na alamta cewar, akwai yiwuwar samun haɗakar ɓangarorin biyu domin tunkarar zaɓen shekarar 2027, abin da wasu ke ganin cewar zai zamewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu alaƙaƙai a zaɓen.