Mutuwa a sanadiyyar zazzabin Lassa a Najeriya ta karu a bana zuwa 151 daga 148, kamar yanda Hukumar Kare Yaduwar Cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sanar.
A rahotonta na mako na 14, NCDC ta ce, an samu rahoton kamuwa da zazzabin Lassa 869 daga jihohi 26 na Najeriya a cikin kananan hukumomi 101 a tsakanin 1 ga watan Janairu zuwa 9 ga watan Afrilu, 2023.
Jimillar korafe-korafen zargin kamuwa da cutar guda 4,555 aka samu a lokacin da hukumar ta kalla.
Cikin korafe-korafe 869 da aka tabbatar a bana, rukunin mutanen da suka fi kamuwa da zazzabin sune ‘yan shekaru 21 zuwa 30.
Hukumar Lafiya ta duniya ta bayyana cewa, zazzabin Lassa wata cuta ce da take samo asali daga kwayar cutar Lassa da ake dauka idan mutane sun yi amfani da abinci ko kayan amfanin gida wadanda suka hadu da fitsarin berayen Mastomys.
Zazzabin Lassa ya kasance annobar cikin gida a kasashen Benin, Ghana, Guinea, Liberia, Mali, Sierra Leone, Togo, da kuma Nigeria, haka kuma ana zargin iya samun cutar a sauran kasashen Afirka ta Yamma.