Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴan Bindiga Sun Shiga Dakin Kwanan Dalibai, Sun Yi Garkuwa Da Dalibai Mata

Ƴan bindiga sun kutsa cikin dakin kwanan ɗalibai na Federal University, Gusau a Jihar Zamfara a yau Lahadi.

Batagarin sun kai samame ƙauyen Sabon Gida ne da ke Bunguɗu inda suka kutsa gidan da daliban suke kwana, suka kulle masu gadinsu su biyu suka kuma kwace musu wayoyin hannunsu kafin daga bisani su yi garkuwa da ɗalibai mata biyu da ke karatu a sashin Microbiology na jami’ar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Ƴansanda a Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya ce,  jami’an ƴansanda sun je wajen da abin ya faru, amma sun samu ƴan bindigar sun riga sun bar wajen tare da waɗanda sukai garkuwa da su.

Ya ce Kwamishinan ƴansandan jihar ya tura ƙarin dakaru domin aikin kuɓutar da waɗanda akai garkuwa da su.

Ya ce, “Saboda haka, Kwamishinan ƴansandan yana roƙon samun ƙarin goyon bayan al’umma domin samun nasarar ƴansanda a yunƙurinsu na kuɓutar da waɗanda akai garkuwa da su.”