Talakawan karkara a faɗin Najeriya na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa, inda rahoton Bankin Duniya na watan Afrilu 2025 ya bayyana cewa kashi 75.5 cikin 100 na mazauna karkara na rayuwa ƙasa da layin talauci, lamarin da ke haifar da matsin tattalin arziki, yunwa da rashin lafiyar da ke ƙara tsananta, kamar yanda DAILY TRUST ta rawaito.
A jihar Kano, manoma sun koka da yadda masu kuɗi daga birane ke ƙwace gonakin su, wanda ke haddasa ƙarancin filin noma da hauhawar farashin abinci; “Mutanen birni suna zuwa da kuɗi, amma talakan karkara bai da ilimin sarrafa kuɗi. Idan ka sayar da gonarka, to ka riga ka rasa,” in ji Danladi Yusuf daga Dawakin Kudu.
A Bunkure, Abubakar Alhaji Musa ya bayyana cewa “Yawancin noman rani yanzu ƴan birni sun mamaye shi, muna dogaro da abin da suka noma, hakan ya kai mu faɗawa turken bauta.”
Uwani Bala daga Warawa ta ce “Mazajenmu suna ƙoƙarin nemo abinci, mu mata kuma muna fama da rashin lafiya saboda rashin abinci mai gina jiki, muna amfani da magungunan gargajiya har sai cuta ta tsananta mana.”
Malama Hafsa Uzairu daga Gwarzo ta bayyana cewa “Abin da ake sayarwa naira 100 a birni yana kai wa naira 120 a nan, amma bamu da kuɗin shiga irin nasu,” tana mai cewa yunwa da zazzaɓin cizon sauro sun zama ruwan dare a gare su.
WANI LABARIN: Matashi Ya Kashe Mahaifinsa Da Adda A Jigawa
A jihar Filato kuwa, Dauda Sunday ya ce “Bayan rashin kuɗin noma kamar takin zamani da magungunan ƙwari, har abinci irin su shinkafa da tumatur sun yi tsada sosai,” yayin da Bashir Ibrahim daga Bassa ya bayyana cewa iyalai da dama sun kasa samun abinci da magani saboda tsadar rayuwa.
A Benue, matakin talauci ya kai jama’a sun koma neman ganyayyaki da sauran abincin da ke zube wa a gindin injinan niƙa, inda Onyeje Edward ta ce “Mun riga mun cinye amfanin gona, yanzu lokacin shuka ne kuma babu irin shuka domin mun sayar don sayen abinci,” yayin da Atule Anthony daga Makurdi ya ce “Ba mu da kuɗin abinci ko magani, mutane na mutuwa saboda yunwa da rashin magani.”
A Kwara, manoma kamar Hassan Muhammad da Yunusa Alhasan sun bayyana cewa suna ƙara yawan aikin gona domin samun abin ci, duk da cewa hakan yana shafar lafiyarsu, suna kuma sayar da amfanin gona da araha saboda ƙarancin masu saye, sannan suna sayen kayan masarufi da tsada.
A Bayelsa, Salmon Adaka, wani masunci daga Foropa, ya ce “Bai kamata gwamnati ta bar mu haka ba, muna rayuwa ne kawai bisa taimakon Allah da kuɗin da muke samu daga kifayen teku,” yayin da wani magini, Saviour Bodmas, ya ce rashin aiki da tsadar kayan gini sun hana ƴaƴansa zuwa makaranta, yana mai kiran gwamnatin Tinubu da ta koyi darasi daga gwamnati irin ta Goodluck Jonathan.
Waɗannan koke-koken da DAILY TRUST ta ruwaito sun nuna yadda hauhawar farashi ke ƙara ruguza rayuwar ƴan Najeriya da ke karkara, fatan a nan shine, ko gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin ceto al’umma daga ƙangin talauci da yunwa?