Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴan Jigawa Na Adawa Da Yunƙurin Gwamnati Na Gina Shaguna Kan Naira Biliyan 3.5 A Kano

Wasu ƴan jihar Jigawa sun bayyana damuwarsu dangane da amincewar majalisar zartarwar jihar na kashe naira biliyan 3.5 don gina shaguna a Kano da kuma ware naira miliyan 500 don masu ƙaro ilimi a jami’o’in ƙasashen waje.

A cikin wata sanarwa da ƙungiya mai zaman kanta ta ELIP-Initiative ta fitar mai taken “Jigawa State Quest for Financial Resilience: A Time for Reflection”, ta ce akwai buƙatar gwamnati ta tsaya, ta sake tunani game da irin waɗannan kuɗaɗe.

“Mu ƴan ƙungiyoyin fararen hula muna kira da a zuba jarin da zai haifar da ci gaba mai ɗorewa da ƙara kuzarin tattalin arziƙi ba tare da dogaro da asusun tarayya ba,” in ji Isa Mustapha, shugaban ELIP.

Sanarwar ta bayyana cewa mafi yawancin kuɗaɗen shiga na jihar na fitowa ne daga harajin PAYE, wanda ya zama wani tsari da ba zai dawwama ba.

WANI LABARIN: An Bindige Jami’in NDLEA Har Lahira Yayin Da Yake Bakin Aiki

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin ta zuba jari a sassan da za su haɓaka arziƙin jihar kamar su sarrafa kayan gona, noma na zamani, kasuwar dabbobi, tashoshin sufuri, da kuma harkar yawon shaƙatawa da fasaha.

“Ƙarin jari a waɗannan ɓangarori zai haifar da ayyuka da dama, ya ƙarfafa amincewar masu zuba jari, kuma ya rage talauci,” in ji sanarwar.

Kungiyar ta ce ware kuɗi har naira miliyan 500 don “extra lesson” ga ɗaliban da ke ƙetare ya haifar da tambayoyi game da cancantar makarantu na cikin gida.

“Yakamata a bincika manufar wannan kashe kuɗi da kuma irin makarantun da za su ci gajiyarsu,” in ji su.

Sanarwar ta buƙaci gwamnati da ta dakatar da irin waɗannan kuɗaɗe har sai an tsara hanya mai ma’ana da haɗin gwiwar masana da jama’a domin ciyar da jihar gaba cikin tsari da gaskiya.