Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴan Majalisa Sun Karɓi Cin Hancin Maƙudan Kuɗaɗe Don Tabbatar Da Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya sun karɓi cin hanci har na $25,000 domin tabbatar da amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya ayyana a Jihar Ribas, kamar yadda rahotanni suka bayyana. 

Binciken PEOPLES GAZETTE ya gano cewa aƙalla ƴan majalisa goma sha ɗaya, ciki har da sanatoci bakwai da ƴan majalisar wakilai huɗu, sun tabbatar da samun waɗannan kuɗaɗe daga manyan jami’an gwamnati domin su goyi bayan cire Gwamna Simi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar Ribas tare da naɗa gwamnatin soja. 

Wani ɗan majalisa, ya shaida wa PEOPLES GAZETTE cewa da dama daga cikinsu sun ƙi halartar zaman majalisar saboda rashin amincewa da dokar ta-ɓacin.

A cewarsa, “Gwamnonin wasu jihohi, musamman daga Borno, sun buƙaci wakilansu da kada su goyi bayan dokar ta-ɓaci a Ribas.” 

A zaman majalisar wakilai da aka yi da safiyar yau Alhamis, daga cikin ‘yan majalisa 360, guda 113 ne kawai suka halarta, lamarin da ya sa aka kasa cimma mafi ƙarancin adadin da ake buƙata (na 120) domin yanke hukunci.

A ƙoƙarinsu na gujewa shan kaye, wasu jiga-jigan gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun fara raba cin hanci.

Bayan tattaunawa da ƴan majalisa 14, guda 11 sun tabbatar da karɓar tayin kuɗaɗen, inda bakwai daga cikinsu suka ce an ba su $25,000 yayin da huɗu suka ce sun karɓi $15,000. 

Wani sanata mai suna Seriake Dickson ne kawai ya tabbatar da cewa bai samu tayin cin hancin ba. 

An ruwaito cewa an fara bai wa ƴan majalisa wannan cin hanci tun misalin ƙarfe 6:15 na yamma a ranar Laraba, lokacin da gwamnatin Tinubu ke fuskantar cikas wajen samun goyon bayan majalisar. 

Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci ne bayan rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da ƴan majalisar dokokin jihar da ke biyayya ga tsohon gwamnan Ribas, Nyesom Wike.

Sai dai matakin ya janyo ce-ce-ku-ce, inda masana doka da ƴan Najeriya da dama suka yi Allah-wadai da shi, suna masu cewa ya saɓawa kundin tsarin mulki.