Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴan-ta’adda 41 Ne Suka Mutu A Faɗan Da Ya Ɓarke Tsakanin Boko Haram Da ISWAP A Borno

Mayaƙan Boko Haram da na ISWAP a ƙalla 41 aka kashe bayan ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan ƙungiyoyin a jiya Laraba a Jihar Borno.

Bayanai sun tabbatar da cewar, mayaƙan ISWAP waɗanda suka je wajen faɗan a kan ƙananan jiragen ruwa, sun farmaki ƴan Boko Haram da ke yankin Bakoura Buduma a wajen Duguri da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.

Kukawa da ke yankin Arewacin Borno, na da nisan kusan kilimita 130 daga birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

KARANTA WANNAN: Dubunnan Mutanen Da Suka Mutu A Dalilin Faɗan Manoma Da Makiyaya

Jaridar VANGUARD ta ce, majiyoyi sun sanar da cewar, ƙazamin faɗan ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙan daga dukkan ɓangarorin ciki har da kwamandojinsu.

Wani da ake kira da Zagazola Makama, ƙwararre a fannin ta’addancin da ke faruwa a yankin Tafkin Chadi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Zagazola ya ce, ƴan ɓangaren Boko Haram sun fi shan wahala a faɗan, wanda kwamandoji da dama suka mutu waɗanda suka haɗa da, Modu Kayi, Abbah Musa, Isa Muhammed, Ibrahim Ali, Kanai Zakariya, Bula Salam, Isuhu Alhaji Umaru, Dogo Salman da Abdulrahman Malam Musa da sauransu.