Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴanbindiga Sun Kashe Sojoji 13 Tare Da Harbo Jirgin Yaƙi A Jihar Neja

Ƴanbindiga sun mamaye mazaɓar Chukuba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, yayin da suka harbo jirgin yaƙi na sojoji tare da kashe matuƙinsa.

Shugaban Ƙungiyar Matasa ta Shiroro, Sani Koki wanda yai magana da ƴanjaridu ta waya a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja ya ce, ɓatagarin sun yi wa sojoji kwanton ɓauna inda suka kashe 13 daga cikinsu a kan titin Zungeru zuwa Tegina a daidai mazaɓar Madaka ta Ƙaramar Hukumar Rafi a jihar.

KARANTA WANNAN: Jirgin Sojan Saman Najeriya Ya Yi Hatsari A Jihar Neja

Koki, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici, ya ce, al’amarin ya faru ne ranar Litinin ta kafin Juma’ar, inda ya ce, mutanen ƙauyen sun yi ƙaura zuwa Erena, abun da ya kira da ƙarin wahala kan wadda suke ciki a baya.

Da yake mayar da martani kan maganar lokacin da aka tuntuɓeshi, Shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalissar Sanatoci, Sanata Sani Musa ya bayyana lamarin a matsayin babban abun takaici, sannan kuma ya yi kira ga gwamnati da ta ɗau matakin gaggawa wajen tura dukkan sojojinta da kayan yaƙinta guraren da ake da matsalar tsaro domin ceton rayuka da dukiyoyin al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba.