Jaridar Hausa - Labaran Cigaban Alumma a Dukkan Fannoni

Ƴansanda Sun Dakatar Tare Da Korar Ƴanfashi A Jigawa

Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta ce, ta dakatar da yunƙurin yin fashi da wasu mutane suka shirya yi a yankin Ƙaramar Hukumar Kazaure da ke jihar.

Rundunar a wata sanarwa da ta saki ta hannun Mataimakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, ASP Abubakar Isah yau Lahadi ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 29 ga watan Satumba, 2023.

Sanarwar ta ƙara da cewar, an sanar da rundunar reshen ofishinta na Kazaure cewar, an ga wasu ɓatagari da ake zargin ƴanfashi ne suna haura katangar gidan wani da ake kira da Bello Aliyu na unguwar Ƴanmakaɗa a Kazaure.

KARIN LABARI: Amurka, Yayin Da Kotun Ta Umarci Jami’ar Chicago Ta Bayyana Wa Atiku Bayanan Karatunsa

Rundunar ta ce, da ta samu wannan sanarwa ne ta tura jami’anta na sintiri, inda suka garzaya wajen da abun ke faruwa, yayin da ɓatagarin suka ga ƴansanda sai suka tsere, ƴansanda suka samu mai gidan Bello Aliyu a ɗaure da igiya.

Kafin isar ƴansandan, ɓatagari sun karɓi mukullin motar mai gidan ƙirar Marsandi tare da loda kayan amfanin gida a cikin motar.

Jami’in ƴansandan, Abubakar Isah ya ce, ɓatagarin ba su gudu da motar ba da kuma kayan da suka loda a cikinta.

Sai dai kuma mai gidan ya ce, bai ga makullin motarsa Marsandi ba, da wayar Tecno da wayar Nokia ba.

ASP Abubakar Isah ya ƙara da cewa, ana iya bakin ƙoƙari wajen ganin an kamo ɓatagarin da suka tsere.